logo

HAUSA

Ci Gaban Kasar Sin, Nasara Ce Ta Duniya Ba Kalubale Ba

2022-11-02 19:27:42 CMG HAUSA

DAGA Fa’iza

Lamuran da suka faru a duniya, sun nuna mana cewa, nasara da ci gaban duniya, sun dogara ne da hadin gwiwa da taimakekeniya da kuma moriyar juna tsakanin kasa da kasa. Don haka, kyashi ko adawa da ci gaban wata kasa, ba zai taba amfanawa duniya ba.

Yadda kasashen yammacin duniya ke alakanta kasar Sin da kalmar “barazana” ko “kalubale”, abun damuwa ne ga zaman lafiya da ci gaban duniya. Nasarar Sin, nasara ce ga daukacin duniya, bisa la’akari da yadda karuwar tattalin arzikinta ko nasarori ko fasahohi ko ci gabanta ke shafar duniya baki daya.

Yayin da suke tattaunawa a makon da ya gabata, sabon Firaministan Birtaniya, Rishi Sunak da shugaban Amurka Joe Biden, sun bayyana cewa, za su hada hannu wajen magance “kalubalen kasar Sin”. Shi ma sakatare janar na kungiyar tsaro ta NATO, Jens Stoltenberg, ya bayyana kasar Sin a matsayin barazana, yayin da yake neman Amurka ta kara taimakawa Ukraine a rikicinsu da Rasha.

Ba mu taba jin inda aka ce kasar Sin ta kitsa juyin mulki a wata kasa ba, haka ma ba mu taba jin cewa Sin ta yi mulkin mallaka ko ci da gumin wasu kasashe ba. Kasar Sin ba ta taba girke sojojinta a wata kasa da sunan kare kanta ba, har ila yau, ba mu taba jin inda aka ce ta yi kutse ko katsalandan cikin harkokin wata kasa ko cusawa wata kasa manufofinta ba. To ya aka yi ta zama barazana ko kalubale?

Ko kadan, bai kyautu wadannan shugabanni su rika ayyana Sin a matsayin barazana ba, domin hakan, bata suna ne, suna nema jan Sin cikin rikicin da su ne suka rura wutar ta. Neman dorawa Sin laifi, ba zai kawar da hankalin duniya daga ainihin wadanda ke da alhakin haifar da rikicin ba. Kasar Sin ba ta taba sauya matsayarta game da batun Rasha da Ukraine ba, wadda ita ce hawa teburin sulhu.

A ganina, yadda ake alakanta ta da barazana ko kalubale, ba komai ba ne face adawa da ci gabanta da nasarori da farin jininta a idon duniya, wanda kuma ta same su ne ta sahihiyar hanya. Don haka, yunkurin shafa mata kashin kaji, ba zai haifar da komai ba illa bayyana ainihin masu laifi.