logo

HAUSA

Li Keqiang ya bukaci a kara karfafa tuntuba tsakanin kasashen SCO

2022-11-01 21:05:25 CMG Hausa

Firaministan kasar Sin Li Keqiang, ya yi kira ga kasashen kungiyar hadin gwiwa ta Shanghai (SCO) da su kara inganta mu’amula da juna wajen tabbatar da dunkulewar yankin da daidaita hanyoyin samar da kayayyaki.

Firaminista Li ya bayyana haka ne, yayin da yake karbar bakuncin taron majalisar shugabannin gwamnatocin kasashen kungiyar SCO karo na 21. (Ibrahim)