logo

HAUSA

Ministocin harkokin wajen Sin da Rasha sun aike da wasikun taya murna ga taron tattaunawa kan yadda al’ummomi ke taka rawar bunkasa huldar Sin da Rasha

2022-11-01 15:58:02 CMG Hausa

Jiya Litinin, kungiyar kawancen kasashen Rasha da Sin ta kira taron tattaunawar kasa da kasa kan batun “yadda mu’amalar al’ummomi ke ba da gudummawar kafuwa, da farfadowa, da raya dangantakar dake tsakanin kasar Sin da kasar Rasha”.

Mamban hukumar siyasa ta kwamitin tsakiyar Jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin, kuma mamban majalisar gudanarwa, kana ministan harkokin wajen kasar Wang Yi, ya aike da wasikar taya murnar bude taron.

Haka kuma, shi ma ministan harkokin wajen kasar Rasha Sergey Lavrov ya aike da wasikar taya murna ga wannan taro. (Maryam)