logo

HAUSA

Dubban mutane ne ke tserewa rikici a Jamhuriyar Demokradiyyar Congo

2022-11-01 11:22:56 CMG Hausa

 

Ta’azzarar rikici a gabashin Jamhuriyar Demokradiyyar Congo, ya raba dubban mutane da muhallansu, inda wasu ke tserewa zuwa kasar Uganda.

Stephane Dujarric, kakakin Sakatare Janar na MDD Antonio Guterres, ya ce jami’an majalisar dake Jamhuriyar Demokradiyyar Congo, sun bayyana musu cewa, rikici a karshen mako tsakanin dakarun kasar da ’yan tawayen M23 a arewacin Kivu, ya yi sanadin karuwar ’yan gudun hijira a sansanin tawagar wanzar da zaman lafiya ta MDD dake Kiwanja.

Stephane Dujarric, ya yi kiyasin cewa, cikin kwanaki 11 da suka gabata, kimanin mutane 50,000 sun rasa muhallansu, ciki har da kusan 12,000 da suka nemi mafaka a Uganda, dake makwabtaka da kasar.

A nasu bangare, shugaban hukumar kungiyar AU, Moussa Faki Mahamat da shugaban kungiyar AU, kana shugaban kasar Senegal Macky Sall, sun yi kira da a tsagaita bude wuta da tabbatar da tsaron fararen hula a kasar.

Har ila yau, sun yi kira da a dawo da huldar diflomasiyya tsakanin Jamhuriyar Demokradiyyar Congo da makwabciyarta Rwanda.

A ranar Asabar ne, gwamnatin Jamhuriyar Demokradiyyar Congo ta sanar da matakinta na korar Jakadan Rwanda a kasar Vincent Karega, bisa zargin kasarsa da tallafawa ’yan tawayen M23, zargin da Rwandar musanta. (Fa’iza Mustapha)