logo

HAUSA

UNICEF: Yara na cikin hadarin gamuwa da mummunan tasirin sauyin yanayi a gabas ta tsakiya da arewacin Afirka

2022-10-31 14:12:40 CMG Hausa

Asusun yara ma MDD UNICEF, ya ce yara kanana dake yankunan gabas ta tsakiya da arewacin Afirka, na kan gaba a duniya wajen yiwuwar fuskantar mummunan tasirin sauyin yanayi.

Wani rahoto da asusun na UNICEF ya fitar a jiya Lahadi, wanda ya maida hankali sosai ga kasar Masar, ya yi karin haske ga halin da yara kanana za su iya shiga a wadannan yankuna, sakamakon tasirin sauyin yanayi.

Rahoton wanda aka fitar gabanin babban taron MDD game da sauyin yanayi ko COP27, wanda birnin Sharm El Sheikh na kasar Masar zai karbi bakunci, ya yi nuni da yadda sauyin yanayi da muhalli ka iya zama babbar barazana ga Masar, da adadin da ya kai maki 7.3 cikin 10, wanda shi ne mafi yawa a daukacin yankin da take.

Rahoton na UNICEF ya kara da cewa, kasashen arewacin Afirka na da kimanin yara kanana miliyan 5.3 dake fuskantar barazanar karuwar dumamar yanayi. Inda cikin shekaru 30 da suka gabata, matsakaicin karuwar zafi ke daduwa, da digiri 0.53 a ma’aunin salsus a duk shekaru 10.

Don haka asusun UNICEF ya yi kira da a gagauta aiwatar da matakan kare yara da matasa masu karancin shekaru, ta hanyar gudanar da dabarun samar da hidimomi ga al’ummu, wadanda za su ba da damar kaucewa mummunan tasirin sauyin yanayi, da shirya darussan wayar da kai game da sauyin yanayi, da tabbatar da an saurari muryoyin masu ruwa da tsaki, an kuma yi aiki da su, kana an baiwa yara da matasa muhimmancin da ya dace a bangaren kashe kudaden shawo kan sauyin yanayi, da sauran manufofi, da albarkatu masu nasaba da wannan muhimmin aiki. (Saminu Alhassan)