logo

HAUSA

Antonio Guterres ya yi Allah wadai da harin birnin Mogadishu

2022-10-31 10:55:59 CMG Hausa

Babban magatakardar MDD Antonio Guterres, ya bayyana matukar Allah wadai da harin ta’addancin birnin Mogadishu, fadar mulkin kasar Somaliya. Cikin sanarwar da kakakinsa ya fitar, Mr. Guterres ya ce ya kadu matuka, da jin mummunan harin na ranar Asabar, ya kuma mika sakon ta’aziyya ga iyalan wadanda harin ya rutsa da su, ciki har da na wasu jami’an MDD, da jami’an gwamnati da al’ummar Somaliya. Ya kuma yi fatan samun sauki cikin gaggawa ga wadanda suka jikkata.

Shi ma shugaban hukumar zartaswar kungiyar AU Moussa Faki Mahamat, ya yi tir da mummunan harin na Mogadishu, yana mai tabbatar da aniyar kungiyar AU, tare da hadin gwiwar tawagarta dake aikin tabbatar da mika mulki cikin lumana a kasar ko ATMIS a takaice, ta tallafawa gwamnatin Somaliya, da al’ummar kasar wajen samun nasarar wanzar da zaman lafiya da tsaro a kasar.

Shugaban kasar Somaliya Hassan Sheikh Mohamud ya bayyana cewa, yayin harin na ranar Asabar, wasu tagwayen bama-bamai sun tarwatse cikin motoci 2 a kusa da harabar ma’aikatar ilimin kasar, lamarin da ya haifar da kisan a kalla mutane 100, da jikkata sama da mutane 300. Ana kuma hasashen karuwar mamata sakamakon munanan raunuka da wasu suka samu sakamakon harin.

Harin na ranar Asabar da aka nufi ma’aikatar ilimi da shi, shi ne mafi muni a Somaliya, tun bayan harin bam cikin wata babbar mota da ya auku a kusa da inda na ranar Asabar din ya wakana yau shekaru 5 da suka gabata.  (Saminu Alhassan)