logo

HAUSA

Adadin mamata ya karu zuwa 132 sakamakon karyewar wata gada a yammacin Indiya

2022-10-31 10:56:38 CMG Hausa

Adadin wadanda suka rasu sakamakon karyewar wata gada a India, ya karu zuwa mutane 132, baya ga wasu da dama da suka jikkata, a jihar Gujarat dake yammacin kasar Indiya.

Rahotanni daga wasu kafofin watsa labarai na kasar sun ce, katangar dake rike da gadar ta kogin Machchhu dake gundumar Morbi, ta karye ne da yammacin ranar Lahadi, kuma jim kadan da aukuwar hakan, ma’aikatan ceto, da masu ba da agajin jin kai sun dukufa, domin ceton rayukan wadanda suka fada kogin.

Kaza lika jaridar “The Tribune” ta kasar ta ce gadar ta karye ne, bayan kwanaki 4 kacal da sake bude ta ga al’umma, bayan yi mata gyaran fuska.

Firaministan Indiya Narendra Modi ya zanta da jami’an gwamnatin sa kan al’amarin, inda ya ba da umarnin aiwatar da dukkanin matakan da suka kamata, na tallafawa wadanda ibtila’in ya shafa.  (Saminu Alhassan)