logo

HAUSA

Luiz Inacio Lula da Silva ya koma mukamin shugaban Brazil

2022-10-31 14:03:32 CMG Hausa

Babbar kotun zabe ta kasar Brazil, ta tabbatar da dan takarar jami’iyyar kwadago, kuma tsohon shugaban kasar Luiz Inacio Lula da Silva a matsayin wanda ya lashe zagaye na biyu na babban zaben kasar da aka kada, inda ya yi nasara kan abokin takararsa na jami’iyyar ’yanci, kuma shugaban kasar mai ci Jair Bolsonaro. Da wannan sakamko Mr. Lula ya zama sabon zababben shugaban kasar ta Brazil.

Bisa kididdigar alkaluman kuri’un da babbar kotun zaben Brazil ta fitar, an ce, cikin jimillar kuri’un da aka kammala, Lula ya samu kaso 50.83%, yayin da Bolsonaro ya samu kaso 49.17% na kuri’un.

Yayin zagayen farko na kada kuri’un da aka yi a ranar 2 ga watan nan, Lula ya samu kuri’u mafi yawa, wadanda suka kai kaso 48.42%, sai kuma Bolsonaro dake biye da shi da yawan kaso 43.2% na jimillar kuri’un.

Bisa ka’idar zaben shugaban kasa ta Brazil, idan ba dan takara da ya samu adadin kuri’un da suka haura kaso 50% a zagayen farko na zaben, wajibi ne a ’yan takara 2 mafiya yawan kuri’u su sake shiga zagaye na biyu na kara kuri’a, kuma wanda ya samu kuri’u mafiya yawa a zagayen shi ne zai zama sabon zababben shugaban kasar.

Sabon shugaban Brazil zai kaddamar da gwamnatinsa ne a ranar 1 ga watan Janairun shekarar 2023 dake tafe, inda zai shafe wa’adin shekaru 4.  (Safiyah Ma)