logo

HAUSA

Manzon kasar Sin game da shirin kwance damara ya soki rahoton binciken matsayin nukiliya na Amurka

2022-10-30 16:39:35 CMG Hausa

Jakadan kasar Sin mai lura da harkokin kwance damara Li Song, ya caccaki sabon rahoton nazari game da fasahar nukiliyar (NPR) da kasar Amurka ta fitar.

A yayin jawabin da ya gabatar a taron kolin farko na babban zauren MDD, Li ya bayyana cewa, rahoton da aka fitar ranar Alhamis, ya nuna yadda Amurka da makamanta na nukiliya suke kallon duniya da ma hulda da ragowar kasashe.

Ya bayyana cewa, daftarin aikin, ya karfafa gasa tsakanin manyan kasashe na duniya da rukuni na yin fito na fito, lamarin dake nuna tunani na nuna danni da babakere da neman cikakken karfi a fannin aikin soja. Kuma wannan ya sabawa burin da duniya ke da shi na hana yakin makaman nukiliya da kaucewa tsari na mallakar makaman nukiliyar.

Don haka, ya yi gargadin cewa, sabuwar dabarar mallakar nukiliya ta kasar Amurka, da manufofi da kuma tsare-tsarenta, ko shakka babu za su yi tasiri mai sarkakiyar gaske, tare da yin mummunan illa ga tsare-tsare na tabbatar da tsaro da zaman lafiyar duniya, baya ga dabarun tsaro tsakanin manyan kasashe gami da kasa da kasa da takaita makaman nukuliya na sassa daba-daban, da kwance damara da tsare-tsaren hana yaduwar makaman nukiliya.

Li ya bayyana cewa, a cikin wannan rahoto na NPR, kasar Amurka ta furta wasu kalamai marasa dacewa da zargi da kuma yada jita-jita marasa tushe game da yadda kasar Sin take zamanantar da karfinta na nukiliya.

Bayanai na nuna cewa, Amurka ta rika bijiro da wasu dabaru da nufin dakile makaman nukiliya na kasar Sin. Kuma kasar Sin ta nuna damuwarta matuka, da ma adawa da irin wannan yunkuri na kasar Amurka. (Ibrahim)