logo

HAUSA

Mummunar ambaliyar ruwa ta shafi miliyoyin mutane a Afrika

2022-10-29 16:07:12 CMG Hausa

 

Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta MDD (UNHCR), ta ce sama da mutane miliyan 3.4, sun rasa matsugunansu, haka kuma wadanda suka ba su mafaka na cikin tsananin bukatar taimako, biyo bayan mummunar ambaliyar ruwa da ake fama da ita a kasashen Nijeriya da Chadi da Niger da Burkina Faso da Mali da Kamaru.

Kakakin hukumar UNHCR Olga Sarrado, ta bayyana yayin wani taron manema labarai jiya a Geneva cewa, ambaliyar ruwa mafi muni cikin shekaru 10 da ta auku a Nijeriya, ta yi sanadin mutuwar daruruwan mutane da raba sama da miliyan 1.3 da muhallansu.

Yayin da a kasashen tsakiyar yankin Sahel da suka hada da Niger da Mali da Burkina Faso, mamakon ruwan sama da ambaliya, sun yi sanadin mutuwar daruruwan mutane da raba dubbai da muhallansu, tare da lalata sama kadada miliyan 1 na gonaki.

Ta’azzarar tasirin matsalar yanayi, musamam a yankin Sahel, ya kara tsananta yanayin fari da ambaliya, da rage amfanin gona da bayar da gudunmuwa ga tabarbarewar ayyukan kula da al’umma a daya daga cikin wurare mafi fama da ‘yan gudun hijira a duniya. (Fa’iza)