logo

HAUSA

Moussa Faki Mahamat ya bukaci a dagewa Zimbabwe takunkumai

2022-10-28 11:20:06 CMG Hausa

Shugaban hukumar zartaswar kungiyar tarayyar Afirka AU Moussa Faki Mahamat, ya yi kira da a dage takunkuman da aka kakabawa kasar Zimbabwe.

Cikin wata sanarwa da aka fitar ga manema labarai da yammacin ranar Laraba, Mahamat ya ce yana sake jaddada kiraye-kirayen da AU ta jima tana yi, na gaggauta dagewa hukumomi, da wasu daidaikun ’yan kasar Zimbabwe takunkuman kasashen yamma ba tare da wasu sharudda ba.

Mr. Mahamat ya kara da cewa, ya damu matuka, da mummunan tasirin da takunkuman ke yi ga harkokin tattalin arziki da zamantakewar al’ummar Zimbabwe, a gabar da ake fama da rikicin makamashi da kamfar abinci a duniya, da kuma yunkurin farfadowa daga annobar COVID-19 da ake ciki.

Tun a farko shekarun 2000 ne kasashen yamma, suka kakabawa Zimbabwe takunkumai, biyowa bayan gyaran fuska da kasar wadda ke kudancin Afirka ta yi ga tsarin mallakar filaye, wanda karkashinsa aka amshe filayen noma dake kauyukan kasar daga tsirarun fararen fata, tare da miyar da su mallakin bakaken fata masu rinjaye. (Saminu Alhassan)