logo

HAUSA

Ta Yaya Za A Kubutar Da Kananan Yaran Amurka Daga Harbe-harben Bindiga

2022-10-28 21:33:53 CMG Hausa

Alkaluman da wata kungiyar kasar Amurka mai zaman kanta ta gabatar a kwanan baya, sun nuna cewa, a cikin watanni fiye da 10 da suka gabata, an yi harbe-harben bindiga sau 260 a makarantun Amurka, adadin da ya kafa tarihi a fannin yawan harbe-harben bindiga a shekara guda a makarantun Amurka. Kana kuma shafin Internet na bayanan harbe-harben bindiga na Amurka ya gabatar da adadin kididdiga cewa, ya zuwa ranar 27 ga wata, kananan yara da matasa 1379 sun rasa rayukansu a Amurka, yayin da wasu 3687 suka jikkata.

Ana mamakin cewa, gwamnatin Amurka ta sha daukar fansa sakamakon mutuwar wani sojinta, da sunan wai kiyaye hakkin dan Adam, amma me ya sa ta kau da kai daga mutuwar dubban kananan yara da matasa cikin harbe-harben bindiga a kasar?

Hakika Amurka ta san abun da ya zama wajibi ta yi, amma ba ta yi kome ba. Idan ‘yan siyasar Amurka suka yi niyyar bauta wa jama’a, biyan bukatun jama’a da tsara manufofi bisa sanin ya kamata, to, za su warware matsalar bindiga, amma ba su yi kome ba, suna kokari tukuru a harkokin siyasa kawai.

Idan Amurka ba ta kyautata tsarin siyasarta ba, kuma masu son kai sun rika samun mukamai a gwamnatin Amurka, sa’an nan masu hannu da shudi sun rika samun riba ta hanyoyin samar da bindiga da tufafi masu sulke, to, da wuya al’ummar Amurka su kare kansu daga harbe-harben bindiga, za su ci gaba da rasa rayukansu. (Tasallah Yuan)