’Yan majalissar dokokin Iraqi sun amince da majalissar zartaswa da Al-Sudani ya gabatar
2022-10-28 11:39:13 CMG Hausa
’Yan majalissar dokokin kasar Iraqi, sun amince da sunayen mutanen da sabon firaministan kasar Mohammed Shia' al-Sudani ya gabatar musu, domin nada su mukaman ministoci.
’Yan majalisar sun kada kuri’ar amincewa da mutane 21 cikin 23 da aka gabatar gabansu, sun kuma dage tattaunawa kan wadanda za a nada ministoci a ma’aikatun muhalli da gidaje, sakamakon sabanin siyasa dake tattare da nadinsu.
Yayin zaman tabbatar da nadin, Al-Sudani ya karanta shirin gwamnatin da zai kafa. Kuma bayan amincewar ’yan majalisar dokokin an rantsar da shi tare da sauran ’yan majilissar zartaswar.
A nasa bangare, shugaban kasar Iraqi Abdul Latif Rashid, ya taya Al-Sudani murnar samun nasara, ya kuma bayyana kwarin gwiwarsa, game da kwarewar sabon firaministan, a fannin tunkarar kalubalen da kasar ke fuskanta. (Saminu Alhassan)