logo

HAUSA

CBN zai fitar da sabbin takardun Naira a tsakiyar watan Disamba

2022-10-27 10:01:37 CMG Hausa

Gwamnan babban bankin Najeriya Godwin Emefiele, ya ce za a fitar da sabbin takardun kudin kasar wato Naira, wadanda aka kara kyautata ingancinsu a ranar 15 ga watan Disamba dake tafe. A cewar gwamnan bankin na CBN, an dauki matakin ne da nufin shawo kan kalubalen dake tattare da zagayawar kudaden kasar a hannun jama’a.

Godwin Emefiele ya shaidawa manema labarai hakan ne a birnin Abuja, fadar mulkin kasar. Yana mai cewa, matakin ya zama wajibi, duba da yadda kasar ke fuskantar manyan matsalolin dake kara habaka, wadanda kuma ke tattare da mummunan sakamako.

Ya ce a kalla kaso 80 bisa dari na kudaden dake yawon hannun jama’a ba sa bi ta bankunan kasuwanci, wanda hakan sakamako ne na yadda wasu ke boye kudaden. A cewar sa hakan ya sa al’ummar Najeriya fuskantar yankewar takardun kudade, da yiwuwar fadadar bazuwar kudaden jabu, kamar dai yadda rahotanni da dama daga jami’an tsaro suka tabbatar. (Saminu Alhassan)