logo

HAUSA

Xi ya taya murnar shirya bikin liyafar shekara-shekara ta kwamitin huldar Amurka da Sin

2022-10-27 13:27:48 CMG Hausa

A jiya Laraba ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya aike da sakon taya murna ga kwamitin kula da hulda tsakanin kasashen Amurka da Sin, bisa shirya bikin liyafar yamma ta ba da lambobin yabo, inda Xi ya taya mataimakin shugaban majalisar kwamitin huldar Amurka da Sin, kana shugaban rukunin ACE Evan G. Greenberg, murnar samun lambar yabo, ya kuma yaba da kokarin da kwamitin da mambobinsa ke yi cikin dogon lokaci, domin raya huldar dake tsakanin kasar Sin da Amurka, da ingiza hadin gwiwar dake tsakanin sassan biyu a fannoni daban daban.

Xi ya yi nuni da cewa, a halin da ake ciki yanzu, kasashen duniya suna fuskantar rashin tabbaci, don haka ya dace kasar Sin da Amurka su kara karfafa hadin gwiwa, da cudanyar dake tsakaninsu, ta yadda za su taka rawa wajen ci gaban duniya, da kuma wanzar da zaman lafiya a fadin duniya. Ya kara da cewa, kasar Sin tana son yin kokari tare da Amurka domin samun ci gaba tare.

Kana shugaba Xi ya yi fatan kwamitin huldar Amurka da Sin, da aminai a fannoni daban daban da suke goyon bayan huldar, za su ci gaba da ba da gudummowa, domin maido da ci gaban huldar sassan biyu yadda ya kamata. (Jamila)