logo

HAUSA

Kasar Ukraine tana bukatar Euro biliyan 4 don shiga lokacin sanyin hunturu

2022-10-26 11:20:25 CMG Hausa

Ministan raya al’umma da yankuna na Ukraine Oleksiy Chernyshov ya bayyana cewa, kasarsa tana bukatar tsabar kudi har euro biliyan 4, kwantankwacin dalar Amurka biliyan 3.97, don shiga lokacin sanyi.

Chernyshov ya shaidawa taron kwararru na kasa da kasa kan sake gina da zamanintar da kasar Ukraine da aka yi a birnin Berlin na kasar Jamus cewa, kasarsa na bukatar wadannan kudade ne, domin gyara gidaje da taimakawa bangaren kiwon lafiya da samar da makamashi.

Ya ce, baya wadannan kudaden, haka kuma Ukraine ba ta da nau’rori na samar da ruwan sha da makamashi, kamar tashohin tsaftace ruwa da na dumama jiki na tafi da gidanka, da injunan samar da wutar lantarki masu amfani da man dizel da na’urorin dumama gida.

Ukraine dai na fuskantar matsalar makamashi, yayin da ake daf da shiga lokacin sanyi, sakamakon rikicinta da Rasha, da suka fara tun a ranar 24 ga watan Fabrairu.

A ranar 18 ga watan Oktoba ne, shugaban Ukraine Volodymyr Zelensky ya bayyana cewa, hare-haren da Rasha ta kaddamar a kan kasarsa, sun lalata kusan kaso 30 cikin 100 na tashoshin wutar lantarkin kasar, lamarin da ya haddasa katsewar wutar lantarki a fadin kasar. (Ibrahim Yaya)