logo

HAUSA

Sunak ya kafa sabuwar majalisar ministocin Birtaniya

2022-10-26 10:26:01 CMG Hausa

Jiya ne, sabon firayin ministan kasar Birtaniya Rishi Sunak ya kafa sabuwar majalisar ministocin kasar, wadda ta kunshi tsoffin ministocin kudi da tsaro da harkokin waje da sauran muhimman mukamai.

Sabbin sunayan ministocin da aka fitar jiya ya nuna cewa, Jeremy Hunt zai ci gaba da zama sakataren kudi, haka ma Ben Wallace zai ci gaba da rike mukamin sakataren tsaron kasa, da James Cleverly wanda zai ci gaba da zama sakataren harkokin waje. Dominic Raab shi ne aka nada a mukamin mataimakin firayin minista kana sakataren shari’a na kasar. Haka kuma an nada Suella Braverman, wadda ta yi murabus daga mukamin ba da dadewa ba, a matsayin sakatariyar harkokin cikin gida, yayin da haka Steve Barclay zai rike mukamin sakataren kiwon lafiya.

Kafin wadannan nade-nade, sai da Rishi Sunak ya samu amincewar kafa sabuwar majalisar ministocin daga sarki Charles III, tare kuma da zama firayin ministan kasar a hukumance. Bayan samun amincewar sarkin ne kuma, ya gabatar da jawabi a gaban ofishin majalisa dake titin Downing na birnin London, fadar mulkin kasar, inda ya bayyana cewa, a halin da ake ciki yanzu, kasar Birtaniya tana fuskantar “mummunan matsalar tattalin arziki”, don haka sabuwar gwamnatinsa za ta mai da hankali kan aikin raya tattalin arzikin kasa domin farfado da imanin da al’ummun kasar suke da shi kan ci gaban kasar. Hakazalika, Sunak ma ya yi tsokaci kan kalubalolin da kasar ke fama da su a cikin gida da kuma ketare, wadanda suka hada da yaduwar annobar cutar COVID-19, inda ya yi alkawari cewa, zai hada kan al’ummun kasar baki daya. (Jamila)