logo

HAUSA

Sojojin Syria sun ce Isra’ila ta kai hari ta sama a yankunan dake kewaye da Damascus

2022-10-25 14:08:27 CMG Hausa

Sojojin kasar Syria sun bayar da wata sanarwa a jiya Litinin cewa, kasar Isra’ila ta kai hari ta sama kan yankunan dake kewayen Damascus, fadar mulkin Syria, lamarin da ya raunata sojan kasar 1, tare da lalata wasu na’urori.

Sanarwar ta ce, da misalin karfe 2 na yammacin Litinin, Isra’ila ta harba rokoki kan wasu sassan dake kewayen Damascus, kuma makaman tsaron saman Syria sun yi nasarar kakkabo wasu rokokin, ko da yake sanarwar ba ta bayyana sunayen sassan da aka kai hare-haren ba.

Kungiyar “Syrian Observatory for Human Rights” mai hedikwata a Birtaniya, ta bayyana cewa, Isra’ila ta yi luguden wuta kan wasu sansanonin soja dake wajen yammacin birnin Damascus.

Tun bayan barkewar yakin basasa a shekara ta 2011 a Syria, sojojin Isra’ila take ta kai hare-hare ta sama kan yankunan Syria, bisa hujjar magance ayyukan sojan kasar Iran. Amma gwamnatocin kasashen Syria da Iran duk sun musunta cewa, Iran ta girke sojojinta a Syria. (Murtala Zhang)