logo

HAUSA

Kusoshin kasashen duniya sun taya Xi Jinping murnar ci gaba da zauna a mukamin babban sakataren kwamitin kolin JKS

2022-10-24 14:23:40 CMG Hausa

Jam’iyyu da manyan jami’an siyasa na kasa da kasa, suna aika sakwanni, ko kuma buga waya, domin taya Xi Jinping murnar ci gaba da zauna a mukamin babban sakataren kwamitin koli na JKS.

Shugaban Rasha Vladimir Putin ya bayyana cewa, shawarwarin da aka yanke a yayin babban taro na wannan karo, za su taimaka wa kasar Sin wajen cimma babban makasudin ci gaban al’amuran tattalin arziki, da kuma kara daga matsayin Sin a duniya. Ya ce, yana fatan kara yin tattaunawa da bunkasa hadin gwiwa na kusa, ta yadda za a inganta ci gaban dangantakar abokantakar hadin gwiwa a dukkan fannoni tsakanin Rasha da Sin.

Shi ma shugaban jam’iyyar ANC mai mulki, kuma shugaban kasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa, cewa ya yi taron wakilan jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin karo na 20, ya nuna hanya mai dorewa da JKS, da kasar Sin suka shiga a sabon mataki. Ya ce jam’iyyar ANC tana daukar dangantakar jam'iyyun biyu da matukar muhimmanci, kuma bisa jagorantar mai girma Xi Jinping, dangantakar da tsakanin jam’iyyar kwaminis ta Sin da ANC za ta kara samun karfafuwa a kai a kai. Yana kuma cike da imani cewa, JKS za ta kara yin hadin gwiwar nagartattun jam’iyyu na kasa da kasa wajen tabbatar da adalci a duniya, da kuma neman ci gaba cikin ruwan sanyi.

Shi ma shugaban jam’iyyar SPLM ta Sudan ta kudu, kana shugaban kasar Salva Kiir Mayardit, ya ce SPLM za ta himmatu wajen gudanar da hadin gwiwa tsakaninta da JKS, da kuma inganta neman ci gaban dangantakar sada zumunta tsakanin kasashen biyu da jam'iyyun biyu.

Bugu da kari, kusoshin kasashen Argentina, da Belarus, da Kazakhstan, da Kyrgyzstan, da Turkmenistan, da Pakistan, da Koriya ta Arewa, da Vietnam, da Laos, da Cuba da dai sauransu, da jagororin jam'iyyun siyasa na kasashen Saliyo da Mauritius da Brazil da sauransu, sun kuma aikawa mai girma shugaban kasar Sin Xi Jinping sakwanni, inda suka taya shi murnar zama babban sakataren kwamitin koli karo na 20 na JKS.   (Safiyah Ma)