logo

HAUSA

’Yan sandan kasar Kenya na farautar mayakan al-Shabab da suka kutsa kai wasu masallatai dake garin Mandera

2022-10-24 10:16:58 CMG Hausa

Rundunar ’yan sandan kasar Kenya, ta ce tana ci gaba da farautar wani gungun mayakan Al-Shabab, da suka kutsa kai cikin wasu masallatai biyu dake garin Mandera lokacin sallar Asubahin ranar Asabar, inda suka gabatar da wasu bayanai ga masallatai.

A cewar kwamandan rundunar ’yan sandan reshen arewa maso gabashin kasar George Seda, rukunin farko na ’yan bindigar su kimanin mutum 5, sun kutsa masallacin Elram A ne dauke da bindigogi kirar AK47, inda suka shaidawa masu halartar sallah a lokacin cewa, suna yaki ne da wadanda ba musulmi ba, don haka suna kiransu da su shiga ayyukan kungiyar. Su kuwa rukuni na biyu sun shiga masallacin Elram B ne kusan sa’i daya da rukunin farko, sun kuma bukaci masallatan da su shiga ayyukan da kungiyar ta Al-shabab ke gudanarwa.

A cewar Seda, ba a samu asarar rayuka ko jikkatar mutane yayin aukuwar wannan al’amari ba. Ya ce yayin da ’yan bindigar ke gabatar da bayanai cikin masallatan, wasu biyu dauke da bindigogi na tsaye a waje suna sanya ido.  (Saminu Alhassan)