logo

HAUSA

Ministan wajen kasar Iran: Matsin lamba daga waje ba zai dakile neman ci gaban Iran ba

2022-10-24 10:15:54 CMG Hausa

Ministan harkokin wajen kasar Iran Hossein Amir-Abdollahian, ya ce matsin lamba, da yada farfaganda daga wasu kasahen waje, ba zai dakile manufofin kasar da al’ummarta na neman ci gaba ba. Amir-Abdollahian ya bayyana hakan ne a jiya Lahadi, yayin zantawarsa ta wayar tarho, tare da takwaransa na Syria Faisal Mekdad.

Wata sanarwa da aka wallafa a shafin ministan wajen na Iran, ta ce ministocin biyu sun tattauna ne game da yanayin dangantakar kasashensu, da halin da ake ciki a yankinsu, da sauran batutuwan kasa da kasa da suka shafi moriyarsu.

A bangarensa Amir-Abdollahian, ya ce gwamnatin Iran da ma daukacin al’ummar kasar, za su ci gaba da tallafawa yunkurin samar da daidaito da tsaron kasashen dake yankin, tare da kalubalantar tsoma hannun kasashen ketare a harkokin gidan yankin. Shi kuwa Mr. Mekdad cewa ya yi kasashen yamma, na ta kokarin haifar da tashin hankali a kasashe masu cin gashin kansu ciki har da Iran, kuma Amurka da kasashen na yamma ba sa fatan ganin ci gaba, da cikakken ’yancin Iran, maimakon haka, sun fi fatan ganin kasar ta shiga rudani tare da dogaro ga wasu. (Saminu Alhassan)