logo

HAUSA

Xi Ya Jaddada Fa’idar Babban Taron Wakilan JKS Na 20

2022-10-23 14:26:13 CMG Hausa


Babban sakataren kwamitin kolin Jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin Xi Jinping, ya bayyana a yau cewa, babban taron wakilan JKS na karo na 20, shi ne babban taro na kara daga turar jam’iyyar, da hada karfi da karfe, da inganta hadin kai da kuma sadaukarwa.

Xi ya bayyana cewa, ya kamata jam’iyyar ta yi wa jama’a aiki ta kuma dogara ga jama’a a kan tafiyar da aka sanya a gaba.

Xi ya ce, ya kamata jam’iyyar ta ci gaba da yi wa kanta gyare-gyare kan wannan tafiya da aka sanya a gaba. Yana mai cewa, kasar Sin za ta kara bude kofarta ga kasashen ketare, da sa kaimi ga zurfafa yin gyare-gyare a gida da bude kofa ga waje a dukkan fannoni. Xi ya lura da cewa, kasar Sin mai wadata, za ta kara samar da damammaki ga duniya baki daya. Kuma kamar yadda kasar Sin ba za ta iya samun ci gaba ita kadai ba, haka ma duniya tana bukatar kasar Sin wajen samun bunkasuwarta.

Ya kuma bayyana cewa, cikin shekaru sama da 40 na zurfafa gyare-gyare a cikin gida da bude kofa ga kasashen waje, kasar Sin ta cimma wasu mu’ujiza guda biyu na saurin ci gaban tattalin arziki da zaman lafiyar al’umma na dogon lokaci.

Xi ya bayyana cewa, tattalin arzikin kasar Sin yana da juriya da dama mai kyau, kuma tushen sa mai karfi ba zai taba sauyawa ba, zai kuma ci gaba da kasancewa bisa yanayi mai kyau da inganci na dogon lokaci.

Ya kara da cewa, za mu yi aiki da sauran al’ummomin kasashe, don daukaka dabi’un bil-Adama na zaman lafiya, da bunkasuwa, da nuna adalci, da demikiradiya da ‘yanci, da kiyaye zaman lafiya a duniya, da bunkasa ci gaban duniya, da ci gaba da gina al’umma mai makomar bai daya ga daukacin bil-Adama. (Ibrahim)