logo

HAUSA

Antonio Guterres ya bayyana matukar bakin ciki game da ambaliyar ruwa da ta shafi sassan Najeriya

2022-10-22 11:48:51 CMG Hausa

Babban magatakardar MDD Antonio Guterres, ya bayyana matukar bakin ciki game da ambaliyar ruwa da ta shafi sama da mutum miliyan 2.8 a sassan tarayyar Najeriya.

Mr. Guterres ya bayyana damuwa game da ambaliyar ruwan ta bana, wadda Najeriya ta shafe shekaru 10 ba ta taba ganin irin ta ba, a matsayin mummunan bala’i, wanda ya haifar da asarar rayukan daruruwan mutane, tare da raba kimanin mutum miliyan 1.3 da muhallansu.

Babban jami’in na MDD ya mika sakon ta’aziyya da jajantawa ga gwamnatin Najeriya, da iyalan wadanda lamarin ya shafa, yana mai jaddada aniyar MDD ta ci gaba da tallafawa gwamnatin kasar, a wannan lokaci mai cike da kalubale. Ya ce asarar kayayyakin more rayuwa da gonaki da ambaliyar ta haifar, ya ingiza karin tsadar rayuwa a sassan kasar.

A wani ci gaban kuma, asusun kananan yara na MDD ko UNICEF, ya ce kaso 60 bisa dari na wadanda ambaliyar ta jefa cikin yanayin jin kai yara ne, wadanda kuma ke fuskantar yiwuwar harbuwa da cututtuka, wadanda ta’ammali da gurbataccen ruwa ke haifarwa, da hadarin nutsewa a ruwa, da karancin abinci mai gina jiki.

Alkaluma sun nuna cewa, ambaliyar ruwa ta shafi jihohi 34 cikin jihohin Najeriya 36, ta kuma hallaka sama da mutane 600, yayin da gidaje kimanin 200,000, ko dai suka tabu, ko suka lalace baki daya. (Saminu Alhassan)