logo

HAUSA

Firaministar Burtaniya ta yi murabus bayan kwanaki 45 kan wannan mukami

2022-10-21 10:27:15 CMG Hausa

Rahotanni daga Burtaniya a cewa, firaministar kasar Liz Truss ta yi murabus, kwanaki 45 kacal bayan nada ta kan wannan mukami, biyo bayan wani shirin tattalin arziki da ya jefa fargaba a kasuwannin hada-hadar kudi a watan da ya gabata, wanda ya raba kan ’ya’yan jam’iyyar Conservative.

Da take jawabi a wajen kofar fadar Downing take titi mai lamba 10 a yammacin jiya, Truss ta amince da cewa, ba ta iya cika alkawuran da ta dauka ba a lokacin take takarar shugabancin jam’iyar, baya da jam’iyyar ta yanke kauna a kanta. (Ibrahim Yaya)