logo

HAUSA

Annobar COVID-19 na ci gaba da kasancewa matsalar lafiyar al’umma ta gaggawa

2022-10-21 14:03:27 CMG Hausa

Jaridar The Guardian ta Birtaniya, ta ruwaito babban masanin cututtuka masu yaduwa na Amurka, Anthony Fauci, na gargadi game da saurin ayyana nasara kan annobar COVID-19, ba kawai saboda nasara ce ta gajeren lokaci ba, sai don akwai nau’in cutar dake ci gaba da kasancewa barazana sannu a hankali, ga miliyoyin mutane.

Anthony Fauci, ya bukaci majalisar dokokin Amurka, ta kaucewa dagula lissafi tare da komawa ga samar da kudin yaki da kwayar cutar da ma nau’inta dake daukar lokaci mai tsawo a jikin mutum, tare kuma da ci gaba da kubucewa masana kimiyya da ma’aikatan lafiya. (Fa’iza Mustapha)