logo

HAUSA

Kasar Sin za ta zurfafa dangantakar abokantaka tsakaninta da sauran kasashe

2022-10-21 15:37:36 CMG Hausa

“Kasar Sin za ta zurfafa dangantakar abokantaka tsakaninta da sauran kasashe bisa ka’idojin nuna adalci, da bude kofa ga waje, da yin hadin gwiwa, domin kara samun moriya tare da sauran kasashe.”in ji shugaba Xi Jinping na kasar Sin.

Cikin rahoton da ya gabatar a yayin bude babban taron wakilan jam’iyyar Kwaminis ta kasar Sin karo na 20, shugaban kasar Sin, kana babban sakataren jam’iyyar, Xi Jinping, ya yi kira da a girmama bambancin al’adu a tsakanin kasashen duniya, da yin mu’amala tsakanin mabambantan al’adu, da koyi da juna, da zaman jituwa bisa tushen daidai wa daida, ta yadda za a tinkari kalubaloli tare. Al’ummomin kasar Sin suna son hada kai da jama’ar sauran kasashe, domin samar da makoma mai haske ga dukkanin bil Adama. (Maryam)