logo

HAUSA

Kasar Sudan ta goyi bayan matakin OPEC+ na rage man da ake hakowa

2022-10-19 10:34:08 CMG HAUSA

 

A jiya ne, kasar Sudan ta sanar da goyon bayan mataki na baya-bayan nan da kungiyar kasashe masu arzikin man fetur da kawayenta (OPEC+) suka dauka, na rage yawan man fetur da suke hakowa.

Wata sanarwar da ma’aikatar harkokin wajen kasar ta fitar ta bayyana cewa, ta bibiyi dalilin da ya sa kungiyar da kawayenta suka rage yawan mai da suke hakowa, da adawar da ake nunawa masarautar Saudiya, da kuma kokarin dora mata laifi kan abin da zai biyo baya kan wannan shawara.

Ta kara da cewa, Sudan a matsayinta ta mambar kungiyar, ta nanata cewa, yanke shawarar rage yawan da ake hakowa, ya samu amincewar dukkan kasashe mambobin kungiyar. Sanarwar ta kuma jaddada cewa, Sudan ta goyi bayan matsayin Saudiya cewa, matsayin da OPEC da kawayenta suka dauka, yana da nasaba da yanayin da tattalin arziki ke ciki, da nufin kiyaye daidaito na samarwa da bukatu a kasuwannin man, da takaita yanayi na rashin tabbas, da bai yi hannun riga da moriyar masu amfani da masu samar da shi ba. (Ibrahim Yaya)