logo

HAUSA

Wakilin MDD: An samu ci gaba a kokarin samar da zaman lafiya a kasar Mali

2022-10-19 10:03:49 CMG HAUSA

 

Wakilin musamman na MDD a kasar Mali Ghassim Wane ya bayyana cewa, an samu ci gaba a kokarin da ake na mika mulki da tabbatar da zaman lafiya a Mali, sai dai kuma ya nuna damuwarsa kan yanayin tsaro a kasar.

El-Ghassim ya shaidawa taron kwamitin sulhun MDD cewa, bayan yarjejeniyar da aka cimma a farkon watan Yuli, tsakanin mahukuntan kasar da kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka (ECOWAS), game da jadawalin mika mulki, an samu gagarumin ci gaba a shirye-shiryen da ake na gudanar da zabuka.

Ya kara da cewa, an dauki matakan da suka dace, na kafa hukumar zabe ta musamman, bayan amincewa da dokar zaben a watan Yuni. Yana mai cewa, tsarin sanya ido kan jadawalin gyaran fuskan da aka yiwa harkokin siyasa da na zabuka, wanda ya shafi bangaren Mali da abokan huldar bangarori da dama da lamarin ya shafa, ya fara aiki a mataki na tsare-tsare da kuma siyasa. Ya zuwa yanzu kwamitin kula da harkokin siyasa ya gama har sau 4. (Ibrahim Yaya)