logo

HAUSA

MDD ta yi kira da a yi gaggawar daukar matakin yaki da talauci a duniya

2022-10-18 10:43:38 CMG Hausa

Sakatare janar na MDD Antonio Guterres ya yi kira da a gaggauta daukar matakan gayara koma bayan da aka samu wajen yaki da talauci a duniya.

Antonio Guterres ya ce, annobar COVID-19 ta jefa miliyoyin mutane cikin kangin talauci, inda ta mayar da hannu agogo baya ga nasarar da aka sha wuyar samu cikin sama da shekaru 4.

A cewarsa, rashin daidaito na kara fadada. Kana rashin aikin yi na illata tattalin arzikin iyalai da na kasa, lamarin dake haifar da hauhawar farashin kayayyakin abinci da makamashi, tare da barazanar shigar da tattalin arziki duniya cikin mawuyacin hali.

Ya ce a lokaci guda kuma, matsalolin yanayi da karuwar rikice-rikice na haifar da wahalhalu masu tsanani, inda mutane matalauta suka fi jin radadin a jikinsu.

Antonio Guterres ya kara da cewa, Ranar Yaki da Talauci ta Duniya, zaburarwa ce ga duniya. Yana mai cewa, dole ne taken ranar na Mutunci a Kowanne Bangare, ya kasance kira domin gaggauta daukar matakan da suka hada da samar da mafita dake mayar da hankali kan jama’a, daga kiwon lafiya zuwa aikin yi da tabbatar da daidaiton jinsi da kare jama’a da sake fasalin tsarukan samar da abinci da ilimi.

Sauran sun hada da daukar matakan sauya tsarin hada-hadar kudi na duniya dake kokarin durkushewa da tabbatar da samar da kudi da dabarun saukaka biyan bashi ga dukkan kasashe da kuma taimakawa kasashe masu tasowa wajen karkata daga amfani da man fetur mai illata yanayi, zuwa makamashin da ake iya sabuntawa da samar da guraben ayyukan yi a bangarori tattalin arziki da suka dace da kare muhalli. Bugu da kari, ya yi kira da a kawo karshen rikice-rikice da shawo kan rarrabuwar kawuna tsakanin yankuna da neman wanzar da zaman lafiya tare da kokarin cimma muradun ci gaba masu dorewa. (Fa’iza Mustapha)