logo

HAUSA

Sakataren MDD ya yi kira da a kawo karshen tashin hankalin dake faruwa a yankin Tigray

2022-10-18 10:15:04 CMG Hausa

Babban magatakardan MDD Antonio Guterres ya yi kira da a kawo karshen yakin da ake gwabzawa a yankin Tigray na kasar Habasha, ciki har da janye sojojin kasar Eritrea.

Ya ce, halin da ake ciki a kasar Habasha yana kara ta’azzara. Tashin hankali da barna, sun kai wani mataki na ban tsaro, an kuma wargaza tsari na zamantakewa.

Ya shaidawa manema labarai a hedkwatar MDD dake birnin New York na kasar Amurka cewa, a shirye MDD take ta tallafawa kungiyar Tarayyar Afirka (AU) ta kowace hanya, don ganin an kawo karshen mummunan yanayin da ake ciki, tamkar mafarki ga al’ummar kasar Habasha.

Ya kara da cewa, “muna bukatar sake dawo da tattaunawa cikin gaggawa, domin cimma matsaya mai inganci ta siyasa kuma mai dorewa. Haka kuma, wajibi ne kasashen duniya su hada kai a halin yanzu, domin samar da zaman lafiya a kasar Habasha.

Ya bayyana cewa, fararen hula na dandana kudarsu. Hare-hare ba kai ba gindi, da suka hada da wuraren zaman jama’a, suna halaka mutanen da ba su san hawa ba balle sauka a kowace rana, inda aka lalata muhimman ababan more rayuwar jama’a da takaita samun muhimman hidimomi a rayuwar yau da kullum.

A don haka, ya bukaci dukkan bangarori, da su sauke nauyin da ya rataya a wuyansu, kamar yadda dokokin jin kai na kasa da kasa suka tanada, da kare fararen hula, gami da ma’aikatan jin kai. (Ibrahim)