logo

HAUSA

WFF ya mayar da hankali kan hada kai da matasa

2022-10-18 10:36:53 CMG Hausa

A jiya ne, aka bude taron dandalin shirin samar da abinci na duniya (WFF) na shekarar 2022, inda aka hallara matasa da dama daga sassa daban-daban na duniya, don ba su damar bayyana ra’ayoyinsu kan yadda za a magance matsalar karancin abinci da duniya ke fuskanta, ta hanyar kirkire-kirkire da fasahar kere-kere.

Hukumar kula da abinci da aikin gona ta MDD (FAO) ce ta dauki nauyin kashi na biyu na taron bisa jigon “Abinci mai kyau, Duniya mai koshin lafiya”. Taron na kwanaki biyar, ya gudana ne a zahiri da kuma ta yanar gizo a hedkwatar FAO.

Daga cikin shugabannin duniya da suka yi jawabi a yayin bude taron a zahiri ko ta yanar gizo, babban darektan hukumar FAO Qu Dongyu, ya lura cewa, akwai yiwuwar matasan za su iya bijiro da wata hanya ta samar da wani yunkuri da duniya za ta magance matsalar karancin abinci.

Qu ya bayyana cewa, suna samar da wani dandali da matasa za su rika bayyana ra’ayoyinsu tare da bayar da shawara gami da sabbin dabaru, kan yadda za a sauya tsarin noma da muke bukata. Yana mai cewa, tilas ne a rika tattaunawa da su. (Ibrahim)