logo

HAUSA

Iran: Goyon bayan zanga-zanga da Biden ya yi, tsoma baki ne cikin harkokin gidan kasar

2022-10-17 10:36:11 CMG HAUSA

 

Ma’aikatar harkokin wajen Iran ta ce shugaban Amurka Joe Biden, ya tsoma baki cikin harkokinta na gida, saboda goyon bayan masu zanga- zanga a kasar da ya yi.

A ranar Asabar ne gidan talabijin na Press na kasar, ya ruwaito kakakin ma’aikatar, Nasser Kanaani na cewa, kamar yadda ya sha yi tun bayan barkewar zanga zanga a kasar, Biden ya tsoma baki cikin harkokinta na gidan, ta hanyar goyon bayan masu zanga zanga.

A cewar Nasser Kanaani, Iran ba ta ba da kai ga takunkumai na rashin imani da barazanar Amurka ba, kuma ba za ta tsorata da manufofinta na tsoma baki kuma marasa ma’ana ba.

Kwana guda kafin nan, Joe Biden ya bayyana cewa, ya yi mamakin kwarin gwiwar jama’a na gudanar da zanga zanga a titunan Iran. Zanga zanga ta barke ne a Iran, biyo bayan mutuwar wata mace mai shekaru 22 mai suna Mahsa Amini, a ranar 16 ga watan Satumba a wani asibitin dake birnin Tehran, bayan ’yan sanda sun kama ta. (Fa’iza Mustapha)