logo

HAUSA

Xi ya yi kira da a bunkasa shirin kyautata muhallin kasar Sin

2022-10-16 13:08:59 CMG Hausa

Yayin bude taron mambobin JKS karo na 20, shugaban kasar Xi Jinping, ya yi kira da a bunkasa shirin kyautata muhallin kasar na Beautiful China Initiative.

A cewar Xi Jinping, girmamawa da runguma da kare halittu, na da matukar muhimmanci ga gina kasar Sin zuwa mai tsarin gurguzu ta zamani ta kowacce fuska.

A don haka, ya bukaci a dauki cikakku kuma ingantattun dabarun karewa da inganta yanayin tsaunuka da yankunan ruwa da dazuka da gonaki da filayen ciyayi da kuma Hamadu.

Ya kara da cewa, kasar Sin za ta bayar da muhimmanci ga kare muhallin halittu da tsimi da amfani da albarkatu yadda ya kamata, da kuma neman ci gaba ta hanyar kyautata muhalli da rage fitar da sinadarin carbon. (Fa’iza Mustapha)