logo

HAUSA

Xi Ya yi bayani kan muhimman nasarori 3 da aka cimma cikin shekaru 10 da suka gabata

2022-10-16 12:25:01 CMG Hausa

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya bayyana a yau Lahadi cewa, cikin shekaru 10 da suka gabata, an samu wasu manyan nasarori 3 masu matukar muhimmanci, wandada suka shiga tarihin JKS da al’ummar kasar.

Xi Jinping ya bayyana yayin bude babban taron mambobin JKS karo na 20 cewa, “Mun cika shekaru 100 da kafuwar JKS, gami da mun shiga wani sabon zamani na gurguzu mai sigar kasar Sin, kuma mun fatattaki kangin talauci baki daya, kana mun kammala ginin al’umma mai matsakaicin ci gaba ta kowanne bangare, wato dai, mun cika burinmu na farko a lokacin da muke murnar cika shekaru 100 da kafuwar JKS.”

A cewarsa, wadannan muhimman nasarori ne da suka shiga tarihi, nasarorin da JKS da al’ummar Sinawa suka yi namijin kokarin cimmawa cikin hadin kai, kuma nasarorin da za su kasance cikin tarihin kasar har abada, wadanda kuma za su yi gagarumin tasiri ga duniya. (Fa’iza Mustapha)