logo

HAUSA

(Sabunta) An bude babban taron wakilan JKS karo na 20

2022-10-16 17:01:26 CMG Hausa

An bude babban taron wakilan jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin JKS karo na 20, da misalin karfe 10 na safiyar yau Lahadi a Beijing, fadar mulkin kasar Sin. Shugaba Xi ya gabatar da muhimmin rahoto a madadin kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis karo na 19.

Rahotonsa ya takaita ayyukan da aka yi a cikin shekaru biyar da suka gabata, da manyan sauye-sauyen da kasar Sin ta samu a shekaru goman da suka wuce, wato bayan babban taron wakilan jama’iyyar kwaminis karo na 18, da tabbatar da ayyukan dake gaban jam’iyyar a sabon zamanin da muke ciki. Wato, tun daga yanzu, babban aikin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin shi ne, hada kai da jagorantar al’ummomin kasar, wajen gina kasar Sin dake bin tsarin gurguzu na zamani mai karfi, da cimma muradun raya kasa, wato zuwa shekara ta 2049, lokacin cika shekaru 100 da kafa Jamhuriyar Jama’ar kasar Sin, inda za’a gina kasar Sin ta zamani mai wadata, da karfi, da dimokaradiyya, da ci gaban al’adu, da hadin kai da kyau.

Jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin ta ayyana wasu muhimman burika biyu wajen samar da ci gaban kasar. An riga an cimma buri na farko, wato zuwa shekara ta 2021, lokacin cika shekaru 100 da kafuwar jam’iyyar kwaminis ta kasar, inda aka gina al’ummar kasar Sin mai matsakaiciyar wadata daga dukkan fannoni. Kana, wannan rahoton da shugaba Xi ya gabatar a yau Lahadi, ya yi hangen nesa, da tsara muhimman ayyukan da za’a gudanar, domin neman cimma buri na biyu, wato zuwa shekara ta 2049, lokacin cika shekaru 100 da kafa Jamhuriyar Jama’ar kasar Sin, inda za a gina kasar Sin dake bin tsarin gurguzu na zamani, da wadata daga dukkanin fannoni.

Rahoton ya ce, kasar Sin ta kama sabuwar hanyar zamanantar da kanta daga dukkan fannoni, kana, shekaru biyar masu zuwa, lokaci ne mafi muhimmanci. Rahoton ya bullo da wasu sabbin dabaru, da tsare-tsare, gami da matakai na neman cimma babban buri na biyu a fannoni da dama, ciki har da samar da ci gaba mai inganci, da inganta horas da kwararru, da tabbatar da jigon al’umma, da inganta rayuwar al’umma, da shimfida zaman jituwa tsakanin dan Adam da muhalli, da kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali, da makamantansu.

Wakilan jam’iyyar, gami da wadanda aka ba su goron gayyata na musamman sama da 2300 sun halarci taron, tare da wasu da ba ’yan jam’iyyar kwaminis din ba da sauransu. Za kuma a rufe taron a ranar 22 ga wata.

A wajen taron, za’a saurara, gami da duba rahoton aiki na kwamitin kolin JKS na 19, da duba rahoton aikin da kwamitin ladabtarwa na kwamitin koli na JKS na 19 ya gabatar. Kana, za’a amince da gyararren shiri na kundin ka’idojin jam’iyyar JKS, da kuma zabar membobin kwamitin kolin jam’iyyar da na kwamitin ladabtarwar jam’iyyar a sabon zagaye.

Jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin mai tarihin shekaru 101, ta shafe tsawon shekaru 73 tana kan karagar mulkin kasar Sin, wato tun kafuwar Jamhuriyar Jama’ar kasar Sin. Babban taron wakilan jam’iyyar, gami da kwamitin kolinta, su ne hukumar koli ta jam’iyyar. A kan gudanar da babban taron wakilan jam’iyyar a duk bayan shekaru biyar.  (Murtala Zhang)