logo

HAUSA

Wakilin Sin ya bukaci a kara zurfafa hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa

2022-10-15 16:21:20 CMG Hausa

Jiya Jumma’a zaunannen wakilin kasar Sin dake MDD Wang Hongbo ya bayyana cewa, gudanar da hadin gwiwa tsakanin kasashe masu tasowa, muhimmiyar dabara ce, a daidai lokacin da suke kokarin raya kasa bisa fifikonsu na musamman, don haka kasar Sin tana tsayawa tsayin daka domin goyon bayan hadin gwiwar, kuma ta yi kira ga kasa da kasa da su hada kai domin kara zurfafa hadin gwiwar.

Wang Hongbo ya fadi haka ne yayin babban taron MDD karo na 77 game da batun “sabuwar ajandar raya birane” da “raya harkokin kasa da kasa”, inda ya yi tsokaci cewa, kasar Sin tana kokari matuka kan aikin taimakawa sauran kasashe masu tasowa domin samun ci gaba tare, yayin da take kokarin raya kanta. Haka kuma kasar Sin tana son hada kai da bangarori daban daban, domin hanzarta aikin aiwatar da ajandar samun ci gaba mai dorewa ta MDD nan da shekarar 2030, ta yadda za a tabbatar da ci gaba mai karfi da inganci ba tare da gurbata muhalli ba a fadin duniya.

Jami’in ya kara da cewa, ya dace tsarin raya kasa na MDD, ya martaba ikon mulki da jagoranci na kasashe masu tasowa, kuma kamata ya yi ya ba su goyon bayan da ya dace, yayin da suke kokarin raya kasashensu, musamman ma a bangarorin kawar da talauci, da samar da abinci da makamashi, da inganta tsarin tafiyar da harkokin kasa, da daga matsayin cudanya ta hanyar yin amfani da fasahohin zamani. (Jamila)