logo

HAUSA

Xi Jinping ya taya murnar kafuwar cibiyar kasa da kasa ta bunkasa kirkire-kirkire da ilimi domin wanzar da ci gaba a fannin sufuri

2022-10-14 16:00:42 CMG Hausa

A ranar yau Jumma’a ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aika wasikar murna taya murnar kafuwar cibiyar kasa da kasa ta bunkasa kirkire-kirkire da ilimi domin wanzar da ci gaba a fannin sufuri ta kasar Sin.

Cikin sakon nasa, Xi Jinping ya bayyana cewa, inganta ci gaba mai dorewa a fannin sufurin duniya, da inganta mu’ammalar kasa da kasa, suna da muhimmanci ga tabbatar da daidaiton sassan samar da dabaru, da inganta ci gaban tattalin arzikin duniya.

Kaza lika kafuwar cibiyar kasa da kasa ta bunkasa kirkire-kirkire da ilimi domin wanzar da ci gaba a fannin sufuri, tamkar jigo ne mai muhimmanci a fannin nuna goyon baya ga aiwatar da ajandar wanzar da ci gaba ta MDD ta nan da shekarar 2030.

Ya ce bangaren Sin yana son yin amfani da cibiyar wajen inganta hadin gwiwar sufurin kasa da kasa, ta yadda hakan zai ba da gudummawa ga inganta shawarwarin ci gaba na duniya, da aiwatar da ajandar shekarar 2030 ta MDD, da inganta gina makomar bai daya ta bil’adama.  

An gudanar da bikin kafuwar cibiyar ne a yau Juma’a a birnin Beijing. (Safiyah Ma)