logo

HAUSA

Kwamitin kolin jam’iyyar JKS ya kira taron wadanda ba ‘yan jam’iyyar ba

2022-10-13 14:14:16 CMG Hausa

Kwanan nan kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, ya kira wani taro na mutanen da ba ‘yan jam’iyyar ba ne a birnin Beijing, inda aka saurari ra’ayoyi, da shawarwari daga wajensu, kan daftarin tattaro ra’ayoyi, na rahoton babban taro karo na 20 na jam’iyyar.

Babban sakataren kwamitin kolin jam’iyyar kwaminis ta kasar Sin, Xi Jinping ne ya jagoranci taron, inda ya gabatar da wani muhimmin jawabi dake jaddada cewa, a sabon zamanin da muke ciki, kuma bisa sabbin bukatu, ya dace jam’iyyar kwaminis da sauran wasu jam’iyyun kasar su kara hadin-kai, don habaka nuna kishin kasa, da tattaro hikimomi da karfi daga kowane bangare, da karfafa gwiwar dukkanin al’ummun kasar, a wani kokari na ci gaba da raya kasar Sin ta zamani dake bin tsarin gurguzu daga dukkan fannoni, da farfado da al’ummar kasar Sin baki daya. (Murtala Zhang)