logo

HAUSA

Asusun IMF ya rage hasashen bunkasar tattalin arzikin duniya na badi zuwa kaso 2.7 bisa dari

2022-10-12 10:21:22 CMG Hausa

 

Asusun ba da lamuni na IMF ya rage hasashen bunkasar tattalin arzikin duniya na shekarar 2023 dake tafe zuwa kaso 2.7 bisa dari, hakan na nuna cewa, asusun ya kara rage mizanin hasashen nasa da kaso 0.2 bisa dari, daga hasashen shekarar ta badi da ya gabatar a watan Yulin bana. A bana kuwa, IMF ya tsaida hasashen nasa ne kan kaso 3.2 bisa dari.

Hasashen wanda ke kunshe cikin rahoton yanayin tattalin arzikin duniya ko WEO, ya bayyana yadda tattalin arzikin duniya ke fama da manyan kalubaloli, yayin da hauhawar farashin kayayyaki ta kai wani mataki da aka jima ba a ga irin ta ba a tarihi, ana kuma fuskantar matsayi a fannin hada hadar cinikayya a mafi yawan yankunan duniya, da tasirin rikicin Rasha da Ukraine, da bazuwar cutar COVID-19, wadanda dukkaninsu sun yi tasiri ga sakamakon hasashen.

Har ila yau, rahoton ya bayyana hasashen ci gaban tattalin arzikin na wannan karo, a matsayin mafi rauni, tun bayan wanda aka fitar a shekarar 2001, in ban da lokacin da duniya ta fuskanci komadar tattalin arziki, da lokacin da ake tsaka da fuskantar bazuwar annobar COVID-19. Hasashen ya kuma nuna yanayin babban koma bayan tattalin arziki da manyan kasashe masu wadata suke fuskanta.

Bugu da kari, rahoton ya yi nuni da yadda aka samu koma baya a fannin karuwar GDPn sassan kasa da kasa cikin rubu’i 2 a jere, wanda zai wanzu tsakanin shekarar nan ta 2022 zuwa farkon shekarar 2023, lamarin da zai shafi kusan kaso 43 bisa dari na kasashen duniya, wato kimanin sulusin jimillar GDPn duniya baki daya. (Saminu Alhassan)