logo

HAUSA

Rundunar sojin Najeriya ta yi nasarar hallaka ’yan bindiga da dama a jihar Kaduna

2022-10-12 10:20:16 CMG Hausa

 

Kakakin rundunar sojojin tarayyar Najeriya Musa Danmadami ya ce, sun yi nasarar hallaka ’yan bindiga da dama a jihar Kaduna dake arewa maso yammacin kasar, sakamakon luguden wuta ta sama da aka yi a mafakar wasu gungun ’yan fashin daji, a yankin karamar hukumar Giwa bayan samun bayanan sirri.

Cikin wata sanarwar da ya fitar a jiya Talata, Danmadami ya ce jiragen soji sun kai farmaki mafakar wasu muggan bata gari a jihar ta Kaduna, bayan da suka tsere daga mafakarsu dake jihar Naija mai makwaftaka.

Ya ce sakamakon ruwan wuta da jiragen soji suka yi, manyan kwamandoji da kananan ’yan bindiga da dama sun kwanta dama, kuma rundunar sojin kasar na fatan al’umma za su taimaka da sahihan bayanai a kan lokaci, don gane da duk wasu ayyukan ’yan ta’adda domin a dauki mataki. (Saminu Alhassan)