logo

HAUSA

Uganda ta yi bikin cika shekaru 60 da samun ‘yancin kai

2022-10-10 11:26:51 CMG Hausa

Shugabannin kasashen yankin gabashin Afrika da suka halarci bikin murnar cikar Uganda shekaru 60 da samun ’yancin kai daga mulkin mallaka, sun yi kira da samun hadin kai tsakanin kasashensu domin gaggauta kyautata rayuwar mazauna.

Shugaban Uganda Yoweri Museveni, wanda ya jagoranci bukukuwan da suka samu halartar shugabannin kasashen gabashin Afrika, ya yi kira da a kara yawan amfanin gona.

Ya kuma jadadda cewa, aikin shimfida bututun danyen man fetur na gabashin Afrika, zai gudana kamar yadda aka tsara.

A nasa bangaren, shugaba William Ruto na Kenya, ya yi kira ga ’yan kasuwa da masu zuba jari, su yi amfani da damar dake akwai na babbar kasuwa da shiyyar ke da ita, wajen samar da abubuwa da kasashe daban daban ke samarwa.

Shi kuwa shugaban Burundi Evariste Ndayishimiye, godewa shugaba Museveni ya yi, saboda gudunmawar da yake bayarwa wajen tabbatar da zaman lafiya a shiyyar.

Bukukuwan da suka hada da maci da wasannin al’adu daban daban, sun kuma samu halartar shugaban Somalia Hassan Sheikh Mohamud da na Sudan ta Kudu Salva Kiir da shugaban yankin Zanzibar na Tanzania, Hussein Ali Mwinyi.

Haka zalika, jami’an diflomasiyya da dama da sauran wasu jami’ai ma sun halarci bukukuwan da suka gudana a wuri guda da Birtaniya ta mikawa Uganda mulki a ranar 9 ga watan Oktoban 1962. (Fa’iza Mustapha)