logo

HAUSA

Ka'idar Sin daya tilo a duniya ke tabbatar da kwanciyar hankali a mashigin tekun Taiwan

2022-10-10 21:15:58 CMG Hausa

Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Mao Ning ta bayyana cewa, manufar Sin daya tak a duniya, ita ce ta ke tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a mashigin tekun Taiwan.

Mao Ning ta bayyana hakan ne Litinin din nan, a yayin taron manema labaran da aka saba shiryawa, tana mai cewa, "Muna shirye don samar da yanayi mai kyau na dinkuwa cikin lumana, amma ba za mu taba barin wata kafa da ‘yan aware za su gudanar da ayyukan ‘yancin kan Taiwan ba." (Mai fassarawa: Ibrahim daga CMG Hausa)