logo

HAUSA

Masanin Birtaniya: Duniya ta amince da ci gaban da Sin ta samu a cikin shekaru 10 da suka gabata

2022-10-10 10:21:19 CMG HAUSA

 

Manazari kana shahararren masani na jami’ar Cambridge ta Birtaniya, Martin Jacque ya shedawa wakilin CMG cewa, a cikin shekaru 10 da suka gabata, Sin ta samu ci gaba na a zo a gani a fannin tattalin arziki da zaman takewa da sauran wasu bangarori 10, abin da ya samu amincewa daga al’ummar duniya baki daya.

Yayin da yake zantawa da ’yan jarida a ranar 16 ga watan Satumba, Martin Jacque ya bayyana babbar ma’anar nasarar yaki da talauci da Sin ta samu, wadda ta zamewa sauran kasashe abin koyi. Ya ce:

“A cikin shekarun da suka gabata, Sin ta samu gagarumar nasara wajen yaki da talauci. Abin dake da ma’ana matuka. Kuma ya baiwa duk fadin duniya wani sako cewa, kawar da talauci baki daya a duniya abu ne mai yiwuwa.”

Yayin da yake tabo maganar kafa kyakkyawar makomar Bil Adama ta bai daya da shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya gabatar, ya ce, wannan ra’ayi ya bayyana babban karfi yayin da ake fuskantar sauyin yanayi na daidaita harkokin duniya, kuma ya samar da wata hanya da ta dace wajen samun wadatar al’ummar Bil Adama. Ya ce:

“A ganina, kafa kyakkyawar makomar Bil Adama ta bai daya muradun daukacin Bil Adama ne. Dole ne mu hada kanmu saboda ganin manyan sauye-sauyen da muke fuskanta, ta yadda za a samu moriya da ci gaba tare. A halin yanzu, ana fuskantar sauyin yanayi da sauran wasu kalubale, ba za a iya warware wadannan matsaloli ta hanyar dogaro da karfin wata kasa daya kadai ba, don haka, ya kamata kasashen duniya su hada kansu. Kafa kyakkyawar makomar Bil Adama ta bai daya ya fidda tafarki mafi dacewa ga samun bunkasuwar duniya cikin hadin kai.” (Amina Xu)