logo

HAUSA

AU ta bude cibiyoyin ayyukan hadin gwiwa domin inganta yaki da al-Shabab a Somalia

2022-10-10 11:22:12 CMG Hausa

Shirin wanzar da zaman lafiya na Tarayyar Afrika a Somalia (ATMIS), ya ce ya bude cibiyoyin ayyukan hadin gwiwa, domin inganta tsare-tsare da hada hannu da sojojin Somalia, yayin ayyukan yaki da kungiyar al-Shabab.

Kwamandan rundunar ATMIS Diomede Ndegeya ya ce, cibiyoyin da aka bude a wuraren da shirye-shiryen zaman lafiya na AU ke gudana, za su ba dakarun kawance damar aiki tare, domin tabbatar da ingancin yakinsu a kan ’yan ta’addar.

Ya kara da cewa, cibiyar JOC dake hedkwatar rundunar ATMIS, za ta hada kai ta hedkwatocin yankuna da rundunar ’yan sanda ta ATMIS da hedkwatar shirin na wanzar da zaman lafiya da dakarun Somalia da sauran hukumomin tsaro, domin samar da sabbin bayanai game da barazanar kungiyar al-Shabab da nasarorin ayyukan rundunonin.

Har ila yau, ya ce cibiyoyin na goyon bayan aiwatar da kudurorin MDD dake bukatar sojojin Somalia su karbi ragamar ayyukan tsaron kasar sannu a hankali.

A nasa bangare, mataimakin ministan tsaron Somalia, Abdifatah Qasim Mahamud ya ce, ayyukan kawance na baya-bayan nan da aka yi a yankunan Hiran da Galgaduud na yankin tsakiyar kasar ta Somalia, sun gudana cikin nasara. (Fa’iza Mustapha)