logo

HAUSA

Ya Kamata Amurka Da Wasu Kasashen Yamma Sun Kalli Laifinsu Na Nuna Wariya Ga ‘Yan Asalin Kasashensu

2022-10-10 09:06:28 CMG HAUSA

DAGA MINA

Abokai, tun kafuwar kasar Amurka a karni na 18, Indiyawan daji ‘yan asalin Amurka suka fara shan wahala. Yau “Duniya a zanen MINA” zai yi bayani ne kan mawuyacin halin da suke ciki yanzu.

Tun lokacin da Christopher Columbus ya gano nahiyar Amurka, Indiyawan daji ‘yan asalin wurin suke fama da kalubaloli da dama. Tun daga karni na 15 zuwa na 20, fararen fata suka yi ta yiwa Indiyawan dajin kisan gilla ba tare da tsayawa ba, har suka raba yaransu da iyalansu, inda ake cin zarafinsu da hana su koyon al’adunsu, lamarin da ya kai ga bacewar al’adun nasu.

Har zuwa karni na 21 da muke ciki a halin yanzu, Indiyawan daji suna fuskantar mawuyancin hali, Amurka da kuma Canada suna kara nuna musu wariya.

Amma, wadannan masu aikata laifin suna zargin sauran kasashe da take hakkin kananan kabilu. Kwanan baya, Amurka da wasu ‘yan tsirarrun kasashe da wakilan kasashen EU sun zargi kasar Sin game da cin zarafin kanana kabilu, zargin ba shi da tushe ko kadan.

Kamar yadda bayanai suka nuna, kabilu 56 ke zaman rayuwa cikin jituwa a yankin Xinjiang. Ana samun bunkasuwar tattalin arzik da kyautatuwar zaman rayuwa da ci gaban al’adu da bin addinai yadda ya kamata a yankin, wannan shi ne abin da jakadun kasashen Larabawa da Afrika da dama dake nan kasar Sin suka amince da shi, sakamakon yadda suka ganewa idanunsu abubuwan dake wakana a yankin.

Abin da ya kamata Amurka da Canada da wasu kasashe su yi shi ne, su duba laifin da suka aikata na kisan gilla ga Indiyawan daji ‘yan asalin wurarensu, da daina nuna bambancin launin fata ga kananan kabilu ciki har da ‘yan asalin Asiya, tare da kawar da rashin adalci a cikin al’lumma, ta yadda kananan kabilu za su samu ‘yanci da bunkasuwa cikin adalci. (Mai zane da rubuta: MINA)