logo

HAUSA

An Yi Zirga-zirgar Da Ta Haura Miliyan 400 Yayin Bikin Kafuwar Jamhuriyar Jama’ar Kasar Sin Na Bana

2022-10-08 16:32:51 CMG Hausa

Ma’aikatar raya al’adu da yawon shakatawa ta kasar Sin, ta ce bisa alkaluman kididdiga, adadin zirga-zirgar da aka yi a cikin gida, yayin bikin ranar tunawa da kafuwar jamhuriyar jama’ar kasar Sin ta bana, ta kai miliyan 422. Kuma cikin ranekun hutun mako guda na wannan biki, an tattara kudaden shiga da yawan su ya kai kudin Sin RMB yuan biliyan 287.2, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 40.45.

Alkaluman sun nuna yadda a yayin hutun, masu yawon bude ido suka fi yin gajerun tafiye-tafiye, yayin da masu shakatawa na cikin gida suka fi ziyartar lambunan shan iska na wajen birane, wadanda suka dauki kaso 23.8 bisa dari, da kauyukan dake kewaye da birane da kaso 22.6 bisa dari, da manyan wuraren shan iska da suka dauki kaso 16.8 bisa dari cikin jimillar wuraren da aka fi ziyarta.

Ma’aikatar sufurin kasar Sin ta ce ta yi hasashen karbar fasinjoji masu tafiye-tafiye, da yawan su ya kai miliyan 255.54, a yayin ranekun hutun na mako guda na wannan biki.  (Saminu Alhassan)