logo

HAUSA

Nijeriya ta shirya tunkarar barazanar tsaro da ka iya bullowa

2022-10-07 16:17:46 CMG Hausa

 

Shugaban kasar Nijeriya Muhammadu Buhari, ya ce kasar ta shirya magance duk wata barazanar tsaro da ka iya bullowa, bisa la’akari da jari mai yawa da ta zuba kan rundunarta ta soji da kuma kayayyakin more rayuwa masu muhimmanci.

Da yake jawabi jiya, yayin wani biki na rundunar sojin kasar a Kaduna dake arewa maso yammacin kasar, shugaban ya ce gwamnatinsa ta zuba kudi mai yawa a fannin ababen more rayuwa, kamar layukan dogo da tituna da tashoshin jiragen ruwa da filayen jirgin sama, har ma da farfado da bangaren makamashi, ta hanyar aiwatar da gyare-gyare masu muhimmanci.

A cewarsa, al’ummar Nijeriya za su iya kwantar da hankalinsu, bisa la’akari da cewa, rundunar sojin kasar za ta iya magance duk wata barazanar tsaro a kowanne bangare na kasar, kamar yadda ta yi a yankin arewa maso gabashin kasar da ke fama da matsalolin ta’addanci.

Shugaba Buhari, ya kuma bukaci rundunonin sojin kasar, su kare muhimman ababen more rayuwa daga masu batawa da marasa kishin kasa da kuma kare karfin tattalin arziki da na sojin kasar.

Da yake bayyana wasu daga cikin shirye-shiryen gwamnatinsa na shirya rundunar sojin ta yadda za iya shawo kan kalubalen tsaro a kasar, ya ce gwamnati ta samar da tsaruka 550 na tattarawa da musayar bayanai ga rundunar sojin ruwa, kuma daga cikinsu, an riga an fara amfani da 319, a matsayin wani bangare na yi wa zirga-zirgar jiragen sojin ruwa garambawul. (Fa’iza Mustapha)