logo

HAUSA

Sojojin Nijeriya sun kashe ‘yan ta’adda 19 cikin makwanni 2

2022-10-07 16:28:12 CMG Hausa

 

Akalla ‘yan ta’adda 19 aka kashe yayin wasu ayyukan yaki da ta’addanci da sojojin Nijeriya suka aiwatar a arewa maso gabashin kasar, cikin makonni 2 da suka gabata.

Kakakin rundunar sojin Nijeriya Musa Danmadami, ya bayyanawa manema labarai a Abuja, babban birnin kasar cewa, sojojin sun kai hare-hare ta sama kan sansanonin mayakan kungiyoyin Boko Haram da ISWAP a garuruwan Kolaram da Bukar Meram na jihar Borno dake arewa maso gabashin kasar.

Ya ce hare-haren sun yi sanadin mutuwar ‘yan ta’adda 19, yana mai cewa sauran sun tsere.

Haka kuma, ya ce yayin hare-haren, sojojin sun ceto wasu fararen hula 14 da ‘yan ta’addan ke rike da su a sansanoninsu.

A cewar Musa Danmadami, a dan tsakanin, an cafke a kalla ‘yan ta’adda 79, yayin da sama da 400 suka mika wuya tare da iyalansu, inda ya ce ana tantance su domin daukar mataki na gaba. (Fa’iza Mustapha)