logo

HAUSA

Wakilin Sin ya yi kira da a samar wa kasar Sudan ta Kudu gudummawa don tabbatar da zaman lafiya da kyautata yanayin jin kai

2022-10-06 16:44:33 CMG Hausa

Wakilin kasar Sin ya yi jawabi a gun taron tattauna rahoton taron majalisar kare hakkin dan Adam ta MDD karo na 51 game da samar da gudummawa ga kasar Sudan ta Kudu a fannonin fasahohi da kara karfinta a jiya cewa, Sin ta yi kira ga kasa da kasa da su samar wa kasar Sudan ta Kudu gudummawa wajen tabbatar da zaman lafiya da kyautata yanayin jin kai.

Wakilin Sin ya bayyana cewa, a kwanakin baya, manyan kungiyoyin kasar Sudan ta Kudu sun cimma daidaito da daddale yarjejeniya kan tsawaita wa’adin gwamnatin wucin gadi ta kasar, kuma kasar Sin tana maraba da wannan batu, ganin yadda ya dace da moriyar jama’ar kasar Sudan ta Kudu tare da taimakawa wajen tabbatar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin. Ko da yaushe Sin na goyon bayan yunkurin shimfida zaman lafiya a kasar Sudan ta Kudu, kana za ta ci gaba da samar da gudummawa ga kasar Sudan ta Kudu wajen inganta tattalin arziki da zamantakewar al’ummar kasar.

Wakilin Sin ya kara da cewa, Sin na tsayawa tsayin daka kan yin shawarwari da hadin gwiwa a tsakanin bangarori daban daban kan batun kare hakkin dan Adam, da nuna adawa da siyasantar da batun da yin matsin lamba ga sauran bangarori kan batun. Sin ta yaba wa gwamnatin kasar Sudan ta Kudu bisa kokarinta na sa kaimi ga tabbatar da hakkin dan Adam, kana ta yi kira ga kasa da kasa da su girmama ikon mulkin kasar Sudan ta Kudu da cikkakun yankunan kasar, da kuma samar da gudummawa ga kasar wajen tabbatar da zaman lafiya da kyautata yanayin jin kai. (Zainab)