logo

HAUSA

AfDB ya amince ya samar da rancen dalar Amurka miliyan 25 ga kanana da matsakaitan masana’antu a Najeriya

2022-10-06 16:22:54 CMG Hausa

 

Bankin raya kasashen Afirka (AfDB) ya amince ya samar da rancen kudi har dalar Amurka miliyan 25, domin rage gibin kasuwanci a Najeriya, ta hanyar samar da albarkacin kudi ga kanana da matsakaitan masana’antu.

A cikin wata sanarwa da bankin ya fitar, ya sanar da cewa, ya amince da samar da dalar Amurka miliyan 15, da tabbacin kudi har dalar Amurka miliyan 10 ga bankin kasuwanci na FSDH dake Najeriya, domin ba da lamuni ga masana’antu na cikin gida.

A karkashin sashin tsayawa masu samun rancen, ko garanti, bankin na AfDB zai kuma ba da tabbaci kusa kaso 100 na hadarin rashin biya daga takardun lamuni da makamantansu na kudade kasuwanci da FSDH ya bayar.

A cewar bankin na AfDB, wannan zai ba da damar tabbatar da hada-hadar kasuwanci, wadda ta samo asali daga FSDH, da cin gajiyar kasuwanci na shigo da fitar da kayayyaki.

Baki daya tsarin zai samar da sama da dalar Amurka miliyan 200 na hada-hadar kasuwanci a bangaori daba-daban, gami da aikin gona da masana’antu, da bangaren makamashi cikin shekaru uku dake tafe. (Ibrahim)